Online counter

Hukumar NYSC ta cika alkawarin da ta dauka wa matashin nan dan Kano da ya rasa hannayen sa.


Matashin nan Nuruddeen Tahir Gwarzo da a bara ya yi hadarin mota daga Taraba zuwa Kano har aka yanke mishi sauran hannu daya da ya rage masa a yau ya tafi Legas domin aikin hannun kamar yadda aka masa alkwari a baya.
Idan za ku iya tunawa Manuniya ta ruwaito a kwanakin baya hukumar NYSC ta kasa ta yi alkawarin sama wa matashin hannun roba wanda za a yinmasa aikin sakawa kuma ya yi rayuwa kamar kowa.
A safiyar yau dai makusantan Matashi Nuruddeen sun bayyana cewa an yi adu'ar tafiyar sa inda jirgin su ya tashi daga Kano zuwa birnin Ikko na jihar Legas domin yin wannan aikin

Post a Comment

0 Comments