Online counter

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN Yadda 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 30 A Karamar Hukumar Batsari Ta Jihar Katsina


sun kone gari guda
A daren jiya Juma'a ne, 'yan bindiga dauke da manyan makami bisa babura sun kashe Mutane ashirin da bakwai har lahira sakamakon wani hari da suka kai a kauyukan Tsawwa da kuma dankar da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina a daren jiya alhamis, kuma suka kone garin Tsawwa.
Wani dan garin Dankar, Malam Sabi'u Abubakar kuma wanda abu ya faru gaban idonsa ya shaidawa RARIYA a lokacin da suka rako gawarwakin mutane takwas, wadanda yan bindigar suka kashe zuwa fadar mai martaba sarkin Katsina domin ganewa idonsa ta'adancin da yan bindiga suka aiwatar a daren jiya.
Sabi'u Abubakar ya cigaba da cewa 'Yan bindigar sun zo ne da misalin karfe biyar da rabi na yammacin jiya, sojoji sun zo garin Dankar domin amsar bindigun da muka amsa hannun su a kofar gidan maigarin, tafiyar su ke da wuya ba a wuci minti talatin ba, sai aka ce mana ga barayi nan zuwa, sama da mashin dari kowane da goyan mutum biyu dauke da bindigogi, na dauke iyalina muka tsere a cikin mota ta, zuwa garin Yauyau. Sai na ji mutane na cewa ga wuta can na ci, aka ce garin Tsawwa ne aka sanyawa wuta.
Malam Sabi'u ya kara da cewa mu baa kona garinmu ba, amma an kashe mana mutane guda tara har lahira, har da karamin yaro, sune muka taho da gawarwakin su nan, mun rufe guda a can Dankar din.
Shima Dan majalisar jihar Katsina, mai wakiltar karamar hukumar Batsari, Alhaji Jabiru Yauyau ya tabbatar da wannan hari, inda ya ce yanzu dai nan ga gawarwakin mutanen garin Dankar su takwas ana masu wanka. Inda su kuwa na garin Tsawwa sun kone mutane goma sha bakwai a rohatan da nake samu daga can garin Tsawwa. Kuma sun sace abinci da kone kananan yara da kuma dabbobi garin baki daya.
Dan majalisar ya ce zuwa yanzu mun samu rahotan sun kashe Mutane sama da ashirin da bakwai. Allah ya musu rahma

Post a Comment

0 Comments