Online counter

ISA ALI PANTAMI BOKO HARAM KO RAYUWAR MUSULMIN AREWA HARAM?


Kulun muka wayi Gari acikin kasar sai wani Abu ya bayyana Wanda zai nuna maka cewa tabbas kasar NaN akwai wani Abu boye mai muni da wata muguwar manufa da wasu suke bin yanki Arew da shi,
Yankin da kashi 99.99 cikin 100% duka mutanene musulmi da suke bin tsarin Addini musulunci,mutane da suke da fadin kasa acikin Najeriya
Wasu sun kirkiri Hanyoyin da za,a tarwatsa yankin Arewa da musulmin Arewa ta hannu "yan uwan mu" yan Arewa da suke wawaye wasu kuma jahilai da basu fahimci Addiniba
Bayani shugaban kungiyar Boko HARAM akan malam pantami da kisan marigayi malam jafar Adam ya nuna cewa kungiyar boko HARAM ta yakine da rayuwar mudulmin Arewa da Arewa baki daya,
Domin su "yan rayuwar musulmi Haranne,dalilina kuwa shine sunce boko Haramne kuma kashi 99.99 na Al,ummar da boko HARAM ta kashe acikin kasar NaN mutanene " yan Arewa kuma musulmi
Bata kyale malaman Addini ba da suke kokarin yada Addini Allah madaukakin sarki ba,basu kyale mutane da suke zuwa niman na Kansu ba,basu kyale masu yin sallah acikin masalaci ba
Yau kuma sun kara fitowa fili sun bayyana manufarsu akan cewa sufa mutanene da sukazo Dan kokarin rusa musulunci da musulmi da suka karbo kwangila,
Kisan malaman Addini da suke yi ya nuna hakan domin duk al,ummar da ta rasa malaman Addini ita wannan Al,umma ta shiga wani Hali kuma
To Ku sani da ikon Allah wannan burin Naku baya chika kuma zamu cigaba da yin Addu,ar Allah ka tarwatsa duk wani azzalumi da yake kokarin kawoma musulunci da musulmi Matsala acikin wannan yankin Namu
Allah kayimana kariya da kariyarka ka tsaremu da tsarewarka ka hana masu mugun nufi cin Narasa abinda suke Nufi akan wannan yakin na Arewa da kasar NaN
Allah kajikan "yan uwan mu musulmi da suka rasa rayukansu akan wannan matsala ka karbi shahadarsu baki daya,su kuma idan suna da rabon shiriya Allah ka shiryar da su
Idan basu da rabo kayimana maganisu da kanka Ameen

Post a Comment

0 Comments