Online counter

Kudin sata: Duk karya ake yi wa Janar Abacha bayan ya mutu Inji Al-Mustapha


Manjo Janar Hamza Al-Mustapha ya karyata zargin da ake jifan tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha, da shi na cewa ya saci makudan dalolin kudi.
Hamza Al-Mustapha ya bayyana cewa a lokacin da Sani Abacha ya dare kan mulki, abin da Najeriya ta mallaka a asusun kudin kasar waje bai da yawa.
A cewar Al-Mustapha, Abacha ya gaji abin da bai kai Dala miliyan 200 ne a asusun kudin kasar waje, amma kafin ya bar mulki ya tara dala tara da ‘yan kai.
Tsohon babban jami’in da ke kula da tsaron Sani Abacha a lokacin da ya ke kan mulki ya ce shugabannin da aka yi a baya ne su ka sace dukiyar Najeriya.
Tsohon Sojan kasar ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka yi hira da shi da safiyar Ranar Alhamis, 6 ga Watan Fubrairun 2020, a gidan rediyon VOA Hausa.
Hamza Al-Mustapha wanda ya yi zaman gidan yari na shekara da shekaru, ya ce an bukaci ya yi wa Muhammadu Buhari irin wannan kazafi da ake yi wa Abacha.
Al-Mustapha ya ce a baya an tursasa masa ya fito ya ce an saci kudin gwamnati a ma’aikatar PTF ta rarar mai da Buhari ya jagoranta a lokacin gwamnatin sojin.
A na sa ra’ayin, da za a fito a yi yaki da rashin gaskiya da gaske, da an kama mutane da yawa an daure a Najeriya. Al-Mustapha ya ce ba da gaske ake yin lamarin ba.

Post a Comment

0 Comments