Online counter

Wani Mutum Ya Shiga Gasar Cin Kwai 50, Ya Mutu Bayan Cinye 41 Akan N10,000


Wani mutum mai shekaru 42 dan asalin jihar Uttar Pradesh ta jihar Indiya mai suna Subhash Yadav ya rasa ranshi bayan yin gasar cinye kwai guda 50.
Rahotanni sun bayyana yadda mutumin ya karbi tayin gasar bayan da musu ya barke a tsakaninshi da wani a kasuwar Bibiganj wanda ta kai sun sanya rupee 2000 (N10,000) ga duk wanda ya iya cinyewa.
Subash ya karbi tayin gasar tare da samun nasarar cinye guda 41, daga nan ne ya shide a kasa wanda hakan tasa mutane sukayi gaggawar kaishi asibiti inda anan ne yace ga garinku nan

Post a Comment

0 Comments